Kungiyar Ansarullah:Kawancen Saudiya Za Su Kwashi Kashinsu A Hanu.
Kakakin Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Muhamad Abdu-Salam ya ce yakin da kawancen Saudiya ta shiga da kasar ya zo musu da ba zata, kuma za su ci gaba da kashe kudadensu ba tare da cin nasara ba.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto Muhamad Abdul-salam kakakin kungiyar Anrasullah ta kasar Yemen a daren jiya asabar na cewa , Sojoji da dakarun sa kai na kasar sun kame wasu sojojin saudiya a yankin Jizan na kudancin Saudiya, kuma duk da karuwar sojojin hayar da sojojinmu ke kamewa, masarautar Ali-sa'oud ba ta dauki abin da mahimanci ba.
Muhamad Abdu-salam ya kara da cewa duk da irin hare-haren wuce gona da irin da kawancen saudiya ke kaiwa kan kasar, al'ummar yemen na ci gaba da kara jajircewa da juriya wajen kalubalantar sojojin hayar saudiya a sassa daban daban na kasar.
A yayin da yakin Yemen din ya shiga shekaru na hudu,jaridar kasar Birtaniya ta nakalto hukumomin saudiya na cewa a cikin shekaru na yaki da kasar Yemen kasar ta kaske sama da bilyan 120 na dalar Amurka.