Pars Today
Da misalin karfe 7 na safiyar yau litinin aka bude cibiyoyin zabe domin kada kuri'a a zaben shugaban kasa na farko ba tare da Robert Mugabe ba.
Tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya sanar da cewar ba zai goyi bayan jam'iyyar Zanu-PF mai mulki ba a zaben shugabancin kasar da za a gudanar.
A Zimbabwe, dubban magoya bayan jam'aiyyun adawa ne suka ne suka gudanar da wata zanga-zanga yau Laraba a Harare babban birnin Kasar, domin jan kunnen gwamnatin kasar akan duk wani yunkurin tafka magudi a zaben kasar dake tafe.
A Zimbabwe, an sanar da mutuwar mutum 2 daga cikin 49 da suka raunana a harin da aka kai a yayin gangamin yakin neman zabe na Shugaban kasar, Emmerson Mnangagwa.
Wani abu ya fashe a yayin da shugaban kasar Zimbabwe yake gudanar da jawabi.
Gwamnatin kasar Zimbabwe na shirin mayar wa turawa fararen fata da gonakinsu da tsohuwar gwamnatin Robert Mugabe ta kwace.
A Zimbabwe 'yan takara 23 ne suka yi rejista a takara zaben neman shugabancin kasar na ranar 30 ga watan Yuli dake tafe, ciki har da shugaban kasar mai ci Emmerson Mnangagwa.
Majalisar dokokin kasar Zimbabwe ta sanar da dakatar da binciken da take gudanarwa kan tsohon shugaban kasar Robert Mugabe bisa zargin hannun da yake da shi cikin bacewar wasu kudaden diamond a kasar da suka kai Dala biliyan 15.
Zimbabwe, za ta shirya manyan zabukanta na farko tun bayan kifar da mulkin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe.
Tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe yaki amsa gayyatar da majalisar dokokin kasar ta yi masa don neman karin bayani dangane da wasu kudade na cinikin diamond da suka kai dala biliyan 15 da suka layar zana a lokacin mulkinsa.