Zimbabwe: Gwamnati Na Shirin Mayar Wa Turawa Da Gonakinsu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31966-zimbabwe_gwamnati_na_shirin_mayar_wa_turawa_da_gonakinsu
Gwamnatin kasar Zimbabwe na shirin mayar wa turawa fararen fata da gonakinsu da tsohuwar gwamnatin Robert Mugabe ta kwace.
(last modified 2018-08-22T11:32:00+00:00 )
Jun 23, 2018 09:13 UTC
  • Zimbabwe: Gwamnati Na Shirin Mayar Wa Turawa Da Gonakinsu

Gwamnatin kasar Zimbabwe na shirin mayar wa turawa fararen fata da gonakinsu da tsohuwar gwamnatin Robert Mugabe ta kwace.

Shirin sabuwar gwamnatin kasar ta Zimbabwe na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta fuskanci koma baya a bangaren noma, sakamakon kasa noma mafi yawan manyan gonakin da aka kwace daga hannun fararen fata.

Gwamnatin ta Zimbabwe za ta mayar da gonakin da aka kwace daga hannun fararen fata amma bisa wasu sharudda, kamar yadda kuma za a iya bayar da hayar gonaki gare su domin nomawa.

Fararen fatar sun yi na'am da wannan mataki, kamar yadda wasu daga cikin bakaken fatar ma suka nuna gamsuwa da hakan, musamman ma leburori masu yin ayyuka a gonakin fararen fata.