Shugaban Kasar Zimbabwe Ya Tsallaka Jiriya Da Baya
(last modified Sat, 23 Jun 2018 19:02:03 GMT )
Jun 23, 2018 19:02 UTC
  • Shugaban Kasar Zimbabwe Ya Tsallaka Jiriya Da Baya

Wani abu ya fashe a yayin da shugaban kasar Zimbabwe yake gudanar da jawabi.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa wani abu ya fashe a daidai lokacin da shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ke kamala jawabinsa a wannan asabar, lamarin da yayi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama.

Kakakin farar Shugaban kasar Zimbabwe ya sanar da cewa babu wani abu da ya samu shugaba Emmerson Mnangagwa  sanadiyar wannan hari.

Wannan hari na zuwa, bayan irinsa da ya faru a safiyar yau assabar a birnin Adis Ababa na kasar Habasha, inda aka bayyana cewa kimanin mutum 83 ne suka sami raunuka sakamakon fashewar wani abu a wajen taron gangamin goyon bayan sabon firayi ministan kasar Ethiopia  Abiy Ahmad da dubun dubatan magoya bayansa suka halarta.

Seyoum Teshome, wanda ya jagoranci shirya gangamin goyon bayan Firaministan kasar ta Habasha a Addis Ababa, ya ce wanda ya kai harin gurnetin, ya yi nufin samun shugaban ne domin hallaka shi, amma jami’an ‘yan sanda suka dakile yunkurin nasa.