Pars Today
Jami'an tsaron kasar Zimbabwe sun yi awun gaba da wasu ministocin tsohuwar gwamnatin Robert Mugabe su biyu saboda zargin rashawa da cin hanci da kuma amfani da mukaminsu don cimma manufa ta kashin kai.
Kamfanin dillancin labarin Reuters ya ambato cewa;shugaban kasa Emmerson Mnangagwa ya amince da kafa gamnatin hadaka tare da jagoran yan hamayya Morgan Tsvangrai.
Tashar telbijin din France 24 ta ambato majiyar tsaron kasar na cewa an nada Constantino Chiwenga a matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar ta Zanu a yau.
Fararen fata manoma a kasar Zimbabwe sun koma gonakinsu a karon farko tun bayan da aka kwace su a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe.
Rundunar 'yan sandan Zimbabwe ta sanar da kame wasu karin tsoffin ministocin kasar biyu kan zargin yin sama da fadi da dukiyar kasa.
Shugaban kasar Zimbabwe ya jaddada shirin gwamnatinsa na janyo masu zuba hannun jari a kasar da nufin bunkasa harkar tattalin arzikin Zimbabwe.
Rundunar Sojojin Kasar Zimbwe Ta Bada Sanarwan kawo karshen karban iko da muhimman wurare a kasar da ta yi wanda ya tilastawa tsohon shugaban kasar Robert Mugabe sauka daga kan kujerar shugabancin kasar.
Jam'iyya mai mulki a kasar Zimbabwe ta ZANU-PF ta sanar da shugaban rikon kwaryar kasar a matsayin dan takararta a zaben shugabancin kasar a shekara ta 2018.
Tsohon shugaban kasar Zimbabwe ya bar kasar zuwa kasar Singapore don gudanar da hutunsa na shekara-shekara, wanda hakan shi ne barinsa kasar na farko tun bayan da aka tilasta masa yin murabus daga shugabancin kasar Zimbabwen.
Wata kotu a kasar Zimbabwe ta dage sauraren shari'ar da a ke yi wa tsohon ministan kudin kasar Ignatius Chombo da ake zargi da rashawa da cin hanci zuwa gobe Alhamis don ci gaba da sauraren batun ba da belinsa da aka gabatar mata.