Zimbabwe: Shugaban Kasa Ya Amince Da Kafa Gwamnatin Hadaka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27039-zimbabwe_shugaban_kasa_ya_amince_da_kafa_gwamnatin_hadaka
Kamfanin dillancin labarin Reuters ya ambato cewa;shugaban kasa Emmerson Mnangagwa­ ya amince da kafa gamnatin hadaka tare da jagoran yan hamayya Morgan Tsvangrai.
(last modified 2018-08-22T11:31:15+00:00 )
Jan 05, 2018 18:58 UTC
  • Zimbabwe: Shugaban Kasa Ya Amince Da Kafa Gwamnatin Hadaka

Kamfanin dillancin labarin Reuters ya ambato cewa;shugaban kasa Emmerson Mnangagwa­ ya amince da kafa gamnatin hadaka tare da jagoran yan hamayya Morgan Tsvangrai.

Dauka wannan matakin da shugaban kasar ta Zimbabwe ya yi, ya zo ne bayan da ya kasa samun cikakken goyon baya daga al'ummar kasar domin cigaba da tafiyar da gwamnati a karkashin jam'iyyar Zanu kawai.

 Emmerson Mnangagwa­ ya haye kan karagar mulkin kasar ta Zimbabwe ne bayan da Robert Mugabe ya yi murabus a karkashin matsin lambar sojoji.

Shekaru 37 Mugabe ya yi akan karagar mulkin kasar, wato tun 1980 da kasar ta sami yanci daga yan mulkin mallakar Birtaniya.

Tsoffin sojojin kasar da suke da bakin fada a ji  a siyasar kasar ta Zimbabwe, sun zargi Mugabe da kokarin nada mai dakinsa akan karagar mulkin kasar.