Mugabe Ya Tafi Kasar Singapore Don Gudanar Da Hutunsa Na Shekara
Tsohon shugaban kasar Zimbabwe ya bar kasar zuwa kasar Singapore don gudanar da hutunsa na shekara-shekara, wanda hakan shi ne barinsa kasar na farko tun bayan da aka tilasta masa yin murabus daga shugabancin kasar Zimbabwen.
Kafafen watsa labaran kasar Zimbabwen sun ce tsohon shugaba Mugaben ya bar kasar ne tare da dukkanin iyalansa da suka hada da mai dakinsa Grace da kuma 'ya'yansa Bona, Robert Junior da kuma Chatunga don gudanar da hutun kana kuma ana sa ran a yayin wannan tafiyar tsohon shugaban zai ga likitocinsa kamar yadda ya saba.
Kasar Singapore dai ita ce kasar da Mugaben ya saba tafiya don duba lafiyarsa musamman batun ciwon idon da yake fama da shi, duk da cewa 'yan adawa sun bayyana cewar cutar da take damunsa ta wuce ta batun ciwon ido.
A kwanakin baya ne dai Mugaben dan shekaru 93 a duniya ya sanar da murabus dinsa daga karagar mulkin kasar Zimbabwen bayan shafe sama da 37 yana mulkin kasar sakamakon matsin lambar da ya fuskanta daga sojojin kasar wadanda suka kwace madafun iko daga hannunsa da kuma yi masa daurin talala.