-
Yeman: Jiragen Saudiyya Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare A Gundumar Ta'iz
Jul 09, 2018 07:27A kalla mutane 6 ne su ka rasa rayukansu sanadiyyar harin jiragen yakin na Saudiyya a yankin shaab al-dakhl a garin Khudair da ke gundumar Ta'iz a kudu maso yammacin Yeman.
-
An Cimma Matsaya Na Sake Dawo Da Alakar Diplomasiya Tsakanin Kasashen Ethiopia Da Eritrea
Jul 09, 2018 02:25Kasashen Ethiopia da Eritrea sun cimma matsaya kan dawo da alakar diplomasiya a tsakaninsu tare kuma da sake buda Ofishin jakadancinsu.
-
Afirka Ta Kudu Ta Jadadda Matsayarta Na Ci Gaba Da Allawadai Da Ta'addancin Isra'ila.
Jul 09, 2018 02:21Gwamnatin Afirka Ta Kudu ta ce ganin yadda HK Isra'ila ke ci gaba da kai hare-haren Ta'addanci kan Al'ummar Palastinu, jakadan kasar ba zai koma birnin Tel-Aviv ba.
-
Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati A Arewacin Marocco
Jul 09, 2018 02:16Dubun dubatan mazauna garin Daru-Baida'a ne suka gudanar da zanga-zangar neman a sako jagororin 'yan adawa na yankin.
-
Mataimakiyar sakataren MDD na ziyara a Nijar
Jul 09, 2018 02:15Mataimakiyar sakataren majalisar dinkin Duniya na ziyara a Jamhuriyar Nijar, inda a jiya Lahadi ta ziyarci Jihar Maradi dake a matsayin cibiyar kasuwancin kasar
-
Hukumar CAF Ta Kori Alkallan Kwallo Da Dama Kan Rashawa
Jul 08, 2018 13:41Kotun da'a ta hukumar kwallon kafa ta Afrika cewa da (CAF) ta kori alkalan kwallon kafa da dama na nahiyar wadanda aka zayyano sunayensu cikin badakalar cin hanci da karbar rashawa.
-
Tunisia : Harin Ta'addanci Ya Kashe Jami'an Tsaro 6
Jul 08, 2018 11:48Hukumomi a Tunusiya sun ce an kashe wasu jami'an tsaron kasar shida a wani harin ta'addanci da aka kai masu a yankin arewa maso yammacin kasar a wannan Lahadin.
-
Nijar Za Ta Ci Gaba Da Karbar Masu Neman Mafaka
Jul 08, 2018 10:18Shugaba Isufu Mahamadu, na Jamhuriya Nijar, ya ce kasarsa zata ci gaba da kasancewa a matsayin kasa ta masu neman mafaka, musamman wadanda MDD, ke kwasowa daga makobciyar kasar Libiya.
-
'Yan Tawayen Sudan Ta Kudu Sun Amince Da Raba Madafun Iko Tsakaninsu Da Gwamnatin Kasar
Jul 08, 2018 07:45Ministan harkokin wajen kasar Sudan ya sanar da cewa: 'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun amince da mika ragamar mataimakin shugaban kasa ga jagoransu Riek Machar a karkashin yarjejeniyar sulhu da aka cimma a kasar.
-
Wani Dan Bindiga Ya Kashe Wani Mai Goyon Bayan H.K.Isra'ila A Kasar Afrika Ta Kudu
Jul 08, 2018 07:44Wani dan bindiga ya aiwatar da kisan gilla kan shugaban jam'iyyar Likud mai mulki a haramtacciyar kasar Isra'ila reshen kasar Afrika ta Kudu.