Mataimakiyar sakataren MDD na ziyara a Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32250-mataimakiyar_sakataren_mdd_na_ziyara_a_nijar
Mataimakiyar sakataren majalisar dinkin Duniya na ziyara a Jamhuriyar Nijar, inda a jiya Lahadi ta ziyarci Jihar Maradi dake a matsayin cibiyar kasuwancin kasar
(last modified 2018-08-22T11:32:05+00:00 )
Jul 09, 2018 06:45 UTC
  • Mataimakiyar sakataren MDD na ziyara a Nijar

Mataimakiyar sakataren majalisar dinkin Duniya na ziyara a Jamhuriyar Nijar, inda a jiya Lahadi ta ziyarci Jihar Maradi dake a matsayin cibiyar kasuwancin kasar

Amina Muhammad, mataimakiyar sakataren majalisar dinkin Duniya na ziyara a Jamhuriyar Nijar, inda a jiya Lahadi ta ziyarci Jihar Maradi don gani da ido, kan irin ayyukan da hukumomin Majalisar ke yi kan hakkokin yara, ilimin mata, kiwon lafiya, da kananan sana’o’in mata sannan da batun canjin yanayi.

A yayin wannan Ziyara, mataimakiyar Saktaren MDD uwar gida Amina Muhamad ta samu kyakkyawar tarbe daga hukumomin jamhoriyar ta Nijer, inda kafin ta fice jahar Maradi ta gana da Shugaban kasar Nijer Muhamadu Issofou.inda a yayin ganawar ta su Shugaba Issoufou ya tabbatar da cewa kasarsa zata ci gaba da kasancewa a matsayin kasa ta masu neman mafaka, musamman wadanda MDD, ke kwasowa daga makobciyar kasar Libiya.

A ranar Asabar 7 ga watan Yuly na shekarar 2018, mataimakiyar sakataren majalisar dinkin duniyar ta soma ziyarar a Jamhuriyar Nijar.

A cewar Amina Muhammad babban makasudin ziyarar shi ne karfafa samar da hakkokin mata a fannonin Ilimi, Lafiya da kuma basu damar shiga al’amuran siyasa wajen tafiyar da al’amuran mulkin kasa.