Nijar Za Ta Ci Gaba Da Karbar Masu Neman Mafaka
Shugaba Isufu Mahamadu, na Jamhuriya Nijar, ya ce kasarsa zata ci gaba da kasancewa a matsayin kasa ta masu neman mafaka, musamman wadanda MDD, ke kwasowa daga makobciyar kasar Libiya.
Kalamman na shugaba Isufu, na zuwa ne a daidai lokacin da wasu kasashen yankin da suka da Mauritania, da ita kanta Libiyar suka amincewa da bukatar kasashen turai na kafa sansanin tantance bakin haure kafin su samu mafaka a turai.
Shugaba Isufu, na bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da wata tawagar MDD da mataimakiyar babban sakatarenta, Amina Mohamed, ta kai a Nijar, inda ya bayyana cewa ''Nijar kasa ce mai karamci, kana mai al'umma masu karamci, zamu ci gaba da karbar mutanen dake cikin wahala, wannan kuma al'ada ce ta kasarmu Nijar''
Saidai shugaban ya gindaya sharadin cewa, kada mutane su kwashe dogon lokaci a kasar, a hanzarta yin komi cikin gajeren lokaci, tare da cewa danganta tallafin kudade Bilyan 1,8 da kungiyar tarayya turai ta baiwa kasar na shawo kan matsalar kwararar bakin haure da cewa ''bai taka kara ya karya ba'', amma duk da hakan ya ce akwai kyakyawar alaka tsakanin kasarsa da kungiyar tarayya Turai da kuma hukumar kula da da kaurar bakin haure ta MDD, cewa da HCR.