Hukumar CAF Ta Kori Alkallan Kwallo Da Dama Kan Rashawa
(last modified Sun, 08 Jul 2018 18:11:55 GMT )
Jul 08, 2018 18:11 UTC
  • Hukumar CAF Ta Kori Alkallan Kwallo Da Dama Kan Rashawa

Kotun da'a ta hukumar kwallon kafa ta Afrika cewa da (CAF) ta kori alkalan kwallon kafa da dama na nahiyar wadanda aka zayyano sunayensu cikin badakalar cin hanci da karbar rashawa.

Matakin hukumar ya hada da korar wasu alkalai kwata kwata, sai kuma wadanda aka haramta wa yin aikin alkalancin ga wasu har na tsawan shekaru da suka kai  goma.

A sanarwar da hukumar ta fitar a shafinta ta zayyana sunayen alkalan da matakin ya shafa, wanda hukuncin mafi tsanani shi ne wanda ya shafi alkalin wasan dan asalin kasar Kenya, Marwa Range, wanda aka dakatar da shi kwata kwata.

Daga shi sai na kasar Gambiya, Ebrima Jallow danaTogo, Yanisu Bebu, wandanda aka dakatar na tsawan shekaru goma goma, na shiga duk wasu harkokin alkalanci a hukumar ta CAF.

Haka kuma akwai wani alkali daga Nijar, mai suna Maman Raja Abba Malan Ousseini, wanda shi kuma aka dakatar dashi na tsawan shekaru 5.

Ko baya da wadanda da akwai wasu alkalai guda 10 galibi daga kasar Ghana wadanda hukumar ta dakatar har sai ta gama bincike kansu.