-
Wasu mahara Sun Kai Hari Cikin Wani Masallaci A Kasar Afrika Ta Kudu
Jun 14, 2018 07:29Wasu mahara sun kai farmaki cikin wani Masallaci a shiyar kudu maso yammacin kasar Afrika ta Kudu, inda suka kashe mutane biyu.
-
Mahukuntan Sudan Da Masar Sun Tattauna Kan Batun Tsaro A Tsakaninsu
Jun 14, 2018 07:15Mahukuntan Masar da Sudan sun gudanar da zaman tattaunawa kan batun karfafa matakan tsaro a tsakanin kasashensu.
-
Rundunar sojin saman Najeriya ta aike da jirage Zamfara
Jun 14, 2018 01:20Rundunar sojin saman Najeriya ta aike da karin jirage biyu ga rundunarta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar zamfara karkashin shirin kai daukin gaggawa ga yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro a jihar Zamfara.Matakin rundunar na zuwa ne a dai dai lokacin da yawan ‘yan gudun hijira da suka kauracewa kauyukansu sakamakon matsalar tsaro a sassan jihar ta Zamfara ke tasamma dubu 10.
-
AU Na Maraba Da Bukatar Sudan Ta Karbar Bakuncin Taron Sulhun Sudan Ta Kudu
Jun 13, 2018 10:44Tarayyar Afrika AU, ta yi maraba da bukatar da Sudan ta gabatar, ta neman karbar bakuncin taro tsakanin shugaban Sudan ta Kudu Salva Kirr da shugaban 'yan adawa na kasar Reik Machar.
-
Sojin Najeriya Sun Hallaka 'Yan Boko Haram 23
Jun 13, 2018 09:47Majiyoyin tsaro a Najeriya sun ce sojojin kasar sun hallaka 'yan mayakan kungiyar Boko haram 23 a wani farmaki da suka kai a yankin tafkin Chadi.
-
Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Ba Zai Tsaya Takarar Shugabancin Kasar Ba
Jun 13, 2018 08:06Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ba zai tsaya takarar shugabancin kasar ba da za a gudanar a wannan shekara ta 2018.
-
Yan Ta'adda Da Yawansu Ya Kai 60 Ne Suka Mika Kansu Ga Jami'an Tsaron Aljeriya
Jun 13, 2018 08:05Ma'aikatar tsaron Aljeriya ta sanar da cewa: Tun daga farkon watan Janairun wannan shekara zuw yanzu 'yan ta'adda da yawansu ya kai 60 ne suka mika kansu ga jami'an tsaron kasar.
-
Majalisar Zimbabwe Za Ta Dakatar Da Binciken Mugabe Kan Kudin Diamond Da Suka Bace
Jun 13, 2018 01:00Majalisar dokokin kasar Zimbabwe ta sanar da dakatar da binciken da take gudanarwa kan tsohon shugaban kasar Robert Mugabe bisa zargin hannun da yake da shi cikin bacewar wasu kudaden diamond a kasar da suka kai Dala biliyan 15.
-
Wasu Mutane Da Yawa Sun Mutu Sakamakon Rikicin Da Ya Barke A Yankin Darfur
Jun 13, 2018 00:58Wasu majiyoyin labarai na kasar Sudan sun bayyana cewar wasu mutane masu yawa sun mutu wasu da dama kuma sun gudu daga muhallinsu sakamakon rikicin da ya barke tsakanin sojojin gwamnati da na masu adawa da gwamnatin a yankin Darfur da ke yammacin kasar ta Sudan.
-
Shugaban E/Guinea Yayi Kira Ga Hadin Kan Kasa Bayan Kokarin Juyin Mulki
Jun 13, 2018 00:57Shugaban kasar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema, yayi kira zuwa da tattaunawa ta kasa don tabbatar da hadin kan kasar don kawo karshen rikici na siyasa da kasar ta shiga ciki tun bayan da shugaban yayi zargin an yi kokarin kifar da gwamnatinsa da kuma dirar mikiyan da jami'an tsaro suka ci gaba da yi wa 'yan adawa.