Rundunar sojin saman Najeriya ta aike da jirage Zamfara
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31704-rundunar_sojin_saman_najeriya_ta_aike_da_jirage_zamfara
Rundunar sojin saman Najeriya ta aike da karin jirage biyu ga rundunarta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar zamfara karkashin shirin kai daukin gaggawa ga yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro a jihar Zamfara.Matakin rundunar na zuwa ne a dai dai lokacin da yawan ‘yan gudun hijira da suka kauracewa kauyukansu sakamakon matsalar tsaro a sassan jihar ta Zamfara ke tasamma dubu 10.
(last modified 2018-08-22T07:01:58+00:00 )
Jun 14, 2018 01:20 UTC
  • Rundunar sojin saman Najeriya ta aike da jirage Zamfara

Rundunar sojin saman Najeriya ta aike da karin jirage biyu ga rundunarta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar zamfara karkashin shirin kai daukin gaggawa ga yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro a jihar Zamfara.Matakin rundunar na zuwa ne a dai dai lokacin da yawan ‘yan gudun hijira da suka kauracewa kauyukansu sakamakon matsalar tsaro a sassan jihar ta Zamfara ke tasamma dubu 10.

Kwamandan rundunar 207 da ke yaki da ayyukan ta’addancin a Zamfara Kaftin Caleb Olayera ta hanyar aiki da jiragen Shalkwaftar ne za a iya kai daukin gaggawa ga yankunan da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.

A cewar kwamandan maimakon jiran karin dakaru daga jihohin Kano da Bauchi yanzu jiragensu za su fara tashi daga birnin Gusau don kai dauki a sassan da ke cikin matsala ta hanyar shawagi a sararin samaniya.

Rundunar dai ta samu karin akalla jirage biyu daga shalkwatarta ta kasa don fatattakar ‘yan bindigar da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar ta Zamfara.

Yanzu haka dai dubban al’ummar jihar ta Zamfara mazauna kauyuka wadanda suka samu tsira da rayukansu daga hare-haren ‘yanbindigar na ci gaba da samun mafaka a biranen jihar.