Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Ba Zai Tsaya Takarar Shugabancin Kasar Ba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31686-shugaban_jamhuriyar_dimokaradiyyar_congo_ba_zai_tsaya_takarar_shugabancin_kasar_ba
Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ba zai tsaya takarar shugabancin kasar ba da za a gudanar a wannan shekara ta 2018.
(last modified 2018-08-22T07:01:58+00:00 )
Jun 13, 2018 08:06 UTC
  • Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Ba Zai Tsaya Takarar Shugabancin Kasar Ba

Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ba zai tsaya takarar shugabancin kasar ba da za a gudanar a wannan shekara ta 2018.

Tashar talabijin ta France 24 ta watsa rahoton cewa: Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Joseph Kabila ya bayyana aniyarsa ta rashin tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben da za a gudanar a cikin wannan shekara ta 2018, kuma zai jinkirta matakin sake tsayawa takarar shugabancin kasar har zuwa bayan shekaru 15 masu zuwa wato bayan wa'adin shugabancin kasa uku a nan gaba.

Tun a ranar 20 ga watan Disamban shekara ta 2016 ce wa'adin shugabancin Joseph Kabila na biyu kuma na karshe ya zo karshe amma ya yi ta jan kafa har zuwa yanzu lamarin da ya janyo dambaruwar siyasa a kasar tare da lashe rayukan mutane masu yawa.