Mahukuntan Sudan Da Masar Sun Tattauna Kan Batun Tsaro A Tsakaninsu
Jun 14, 2018 07:15 UTC
Mahukuntan Masar da Sudan sun gudanar da zaman tattaunawa kan batun karfafa matakan tsaro a tsakanin kasashensu.
A zaman tattaunawan da ya gudana a tsakanin jakadan Masar a Sudan Usamah Shaltut da ministan harkokin cikin gidan kasar Sudan Ibrahim Mahmud Hamid a birnin Khartum a jiya Laraba sun tattauna batun karfafa alakar tsaro a tsakanin kasashensu musamman a fagen yaki da fataucin bil-Adama, fataucin muggan kwayoyi, ayyukan leken asiri a kafafen sadarwa da sauran muggan laifuka da suke addabar kasashen biyu.
Kamar yadda zaman tattaunawan jami'an biyu ya tabo batun kogin Nilu da hanyoyin da suka dace a bi wajen saukakawa al'ummun kasashen biyu amfana da kogin a tsakaninsu.
Tags