-
An Hallaka 'Yan Tawaye 9 A Kudancin Mozambique
Jun 04, 2018 01:57Jami'an 'yan sandar kasar Mozambique sun sanar da hallaka 'yan tawaye 9 a kudancin kasar
-
Aljeriya Ta Kira Jakadan Kungiyar Tarayyar Turai.
Jun 04, 2018 01:56Ma'aikatar harakokin wajen kasar Aljeriya ta kira jakadan kungiyar tarayyar Turai dake cikin kasar domin bayyana rashin jin dadinta game da wani faifan video na cin mutuncin Shugaban kasar Abdul-Azez Boutelfika.
-
Kungiyar ICG Mai Sanya Ido Kan Tashe-Tashen Hankula Ta Nuna Damuwa Kan Rikicin Kamaru
Jun 03, 2018 14:43Kungiyar kasa da kasa mai sanya ido kan tashe-tashen hankula a duniya ta International Crisis Group ta ce; Tashe-tashen hankula a kasar Kamaru suna ci gaba da lashe rayukan mutane.
-
Jami'an Tsaron Kasar Aljeriya Sun Halaka 'Yan Ta'adda 24 A Cikin Wata Guda Kacal
Jun 03, 2018 14:34Ma'aikatar tsaron Aljeriya ta sanar da cewa: A cikin wata guda kacal jami'an tsaron kasar sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda 24 a sassa daban daban na kasar.
-
Najeriya : An Kashe Mayakan Boko Haram 10 A Borno
Jun 03, 2018 07:38Majiyan sojojin Nigeria a jihar Borno na tarayyar Najeriya ta bayyana cewa sojojin kasar sun kashe mayakan kungiyar boko haram 10 mahaya dawaki a wani fafatwa da su ka yi da su a garin Ngelkona na karamar hukumar Ngala a jiya Asabar.
-
An Gudanar Da Zanga Zangar Yin Allah Wadai Da Canza Kundin Tsarin Mulkin A Kasar Komoro
Jun 03, 2018 07:37Jam'iyyun Adawa a kasar Komorro sun gudanar da zanga zangar yin Allah wadai da shirin gwamnatin kasar na gudanar da zaben raba gardama don gabatar da sauye sauye a cikin kundin tsarin mulkin kasar.
-
Majalisar Dokokin Nijar Ta Kammala Zamanta Kan Dokoki
Jun 03, 2018 01:23Majalisar dokokin Jamhuriya Nijar ta kammala zamanta na musamman kan dokoki.
-
Mali : 'Yan Sanda Sun Murkushe Masu Zanga-zanga A Bamako
Jun 03, 2018 01:23'Yan sanda a Mali, sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma lulake, wajen murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Bamako babban birnin kasar.
-
DRC : An Gano Wasu Mutum 5 Da Ake Zaton Sun Kamu Da Ebola
Jun 03, 2018 01:19Hukumomin lafiya a Jamhuriya Demokuraddiyar Congo, sun ce an gano wasu sabbin mutane biyar da ake zaton sun kamu ne da mahaukaciyar annobar nan ta Ebola a arewa maso gabashin kasar.
-
Najeriya : An Sake Kashe Mutum 23 A Jahar Zamfara
Jun 02, 2018 13:53Wasu 'yan bindiga dake zarkin masu fashin shanu sun sake afkawa wani kauye a jihar Zamfara tare da kashe akalla mutum 23 a ranar juma'a.