Najeriya : An Kashe Mayakan Boko Haram 10 A Borno
Majiyan sojojin Nigeria a jihar Borno na tarayyar Najeriya ta bayyana cewa sojojin kasar sun kashe mayakan kungiyar boko haram 10 mahaya dawaki a wani fafatwa da su ka yi da su a garin Ngelkona na karamar hukumar Ngala a jiya Asabar.
Jaridar sahara reporters ta nakalto Onyema Nwachukwu, mataimakin daractan watsa labarai na rundunar "Operation Lafiya dole" yana fadara haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa mayakan na boko haram suna haye kan dawakai a lokacin da suka shiga fafatawa da rundunar sojojin Nigeria tare da taimakon tokororinsu na kasar Kamaru, inda suka rinjayi mayakan na boko haran suka kuma kashe 10 daga cikinsu suka kwace bindigar AK 47 guda biyu daga hannunsu.
Onyema Nwachukwu, ya kara da cewa banda bindigar AK 47 da suka kwace a hannun mayakan na boko haram akwai tutar boko haram, wayoyin sallula biyu da kuma International passport na kasar kamaru guda sannan da kudade da suka samu a hannunsu..