Majalisar Dokokin Nijar Ta Kammala Zamanta Kan Dokoki
Majalisar dokokin Jamhuriya Nijar ta kammala zamanta na musamman kan dokoki.
Kimanin dokoki 45 ne majalisar ta amince dasu a zamanta na tsawan watanni uku, wanda kuma shi ne na farko a wannan shekara ta 2018.
To saidai majalisar ba ta dubi batun dokar harajin nan ba ta kasafin kudin kasar na bana ba, wanda ya haddasa tsakun-tsaka tsakanin gwamnati da wasu kungiyoyin farar hula.
Yanzu dai majalisar ta shiga zaman hutu na wasu watanni uku nan gaba, abun da ke nuni da cewa alkalami ya riga ya bushe ga yunkurin da kungiyoyin fara hula ke yi na ganin an janye dokar ta haraji dake kunshe a kasafin kudin kasar na bana.
Jagororin kungiyoyin fara da dama ne dai ake tsare da gabanin wani yunkurinsu na sake fitowa wata zanga-zanga da mahukuntan birnin Yamai suka haramta kan nuna adawa da sabuwar dokar da suka ce ta takura wa masu karamin hali ne a kasar.