Najeriya : An Sake Kashe Mutum 23 A Jahar Zamfara
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31370-najeriya_an_sake_kashe_mutum_23_a_jahar_zamfara
Wasu 'yan bindiga dake zarkin masu fashin shanu sun sake afkawa wani kauye a jihar Zamfara tare da kashe akalla mutum 23 a ranar juma'a.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 02, 2018 13:53 UTC
  • Najeriya : An Sake Kashe Mutum 23 A Jahar Zamfara

Wasu 'yan bindiga dake zarkin masu fashin shanu sun sake afkawa wani kauye a jihar Zamfara tare da kashe akalla mutum 23 a ranar juma'a.

Wasu kafafen yada labarai na jihar Zamfara dake arewacin Najeriya sun habarta cewa a jiya juma'a wasu 'yan bindiga da ake zaton cewa barayin shanu ne sun sake afkawa kauyenZaloka da ke cikin karamar hukumar Anka, inda suka kashe mutum 23 tare kuma da cinnawa gidajen kauyen wuta.

A cewar shugaban karamar hukumar Anka Alhaji Mustafa Muhammad Anka tuni aka yi jana'izar mutane 23 da maharan suka kashe, sannan ya ce maharan sun bar sako cikin wasika, to saidai bai bayyana sakon da wasikar ta kumsa ba.

A watan Maris da ya gabata, an kai irin wannan mutunan hari kauyen Bawar Daji dake kusa da garin na Zakola, inda maharar suka yi mutane 28 yankan rago.

Jihar Zamfara ta jima  tana fuskantar hare-hare daga maharan da ake zargi 'yan fashi ne da barayin shanu.

Masu sharhi kan harakokin  tsaro na ganin matakan da gwamnati take dauka ba su yi wani tasiri ba na hana ci gaba da kai hare-hare a jihar.