Pars Today
Kungiyar tarayya Afirka (AU) ta yi kira ga bangarori a Aljeriya dasu tattaunada juna domin cimma daidaito akan matakin da shugaban kasar ya dauka na janye wa daga takara shugaban kasa a karo na biyar.
Babban lauya mai zaman kansa Femi Falana ne ya yi wannan kiran ga hukumar zaben kasar mai zaman kanta ( INEC) wacce ya bayyana da cewa tana da wannan iko a karkashin doka.
Dubun dubatan al'ummar kasar Sudan Ne Suka gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati a yankuna da dama na kasar
Wasu 'Yan bindiga sun hallaka fararen hula 13 a arewacin kasar Mozambique
Shugaba Omar al-Bashir na kasar Sudan ya bayyana fatansa na inganta huldar dake tsakanin kasarsa da kuma kasar Rasha.
Fitaccen dan hamayyar siyasar kasar Demokradiyyar Congo ya fito daga gidan kurkuku.
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari akan wani sansanin sojan Mali da yake a tsakiyar kasar tare da kashe sojoji 16.
Rundunar Sojin Burkina Faso ta kaddamar da bincike kan zargin da kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta yi kan wasu dakarunta, na yiwa wasu fararen hula kisan gilla ba da hakki ba.
Gwamnatin kasar Zimbabwe ta sanar da cewa akalla mutane 115 ne ake sa ran sun rasa rayukansu a wata guguwar Iska da ta taso a yankunan gabashin kasar.
Hukumar lafiya ta Duniya (WHO), ta bayyana fatanta na ganin an kawo karshen annobar Ebola a Congo Kinshassa a cikin watanni shida masu zuwa.