Mar 17, 2019 05:34 UTC
  • WHO Ta Ce An Samu Sassauci Game Da Annobar Ebola A Congo

Hukumar lafiya ta Duniya (WHO), ta bayyana fatanta na ganin an kawo karshen annobar Ebola a Congo Kinshassa a cikin watanni shida masu zuwa.

Da yake sake sanar da hakan, babban daraktan hukumar ta (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, yanzu an samu sassauci game da annobar cutar a kasar Congo Kinshasa.

A hannu guda kuma, ya ce, duk da harin da wasu dakaru masu dauke da makamai suka kai kan wasu cibiyoyin rigakafi da shawo kan cutar, hukumar ta WHO ba za ta janye daga kasar ba.

Babban daraktan ya bayyana haka ne a yayin taron manema labarai a Geneva, yana mai cewa, a watan Agustan bara ne, cutar ta barke karo na 10 a tarihin kasar ta Congo Kinshasa.

Yanzu haka hukumar WHO da abokan huldarta na tafiyar da wasu cibiyoyin yin rigakafi da shawo kan cutar a yankunan dake fama da cutar domin taimakawa kasar kawar da wannan cuta.

Tags