An Sallami Fitaccen Dan Hammaya Siyasar Congo
(last modified Sun, 17 Mar 2019 18:43:57 GMT )
Mar 17, 2019 18:43 UTC
  • An Sallami Fitaccen Dan Hammaya Siyasar Congo

Fitaccen dan hamayyar siyasar kasar Demokradiyyar Congo ya fito daga gidan kurkuku.

A jiya Asabar ne fitaccen dan siyasar kuma shugaban jam’iyyar Lumumba Progressive Movement, Franck Diongo ya sami kyakkyawar tarba daga magoya bayansa, bayan fitowarsa daga kurkukun Makala.

M. Diongo dai yana cikin fursunonin siyasar da shugaban kasar Felix Tshishekedi ya yi wa afuwa bayan hawansa karagar mulki.

Tun a 2016 ne aka daure Diongo na tsawon shekaru 5 a gidan kurkuku.

Mahaifin Diongo ya bayyana cewa; An kama shi ne saboda dalilai na siyasa, amma babu wani laifin da ya aikata.

 Wannan dai na daga cikin alwashin da Shugaban kasar Tshisekede ya yi na sako dukkanin fursunonin siyasar kasar, musamman wadanda aka kame a lokacin Zanga-zangar 30 ga watan Disamba.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil’adama suna zarginsa da fuska biyu akan hakkin dan’adam, saboda ana ci gaba da kame masu rajin kare hakkin bil’adama a karkashin gwamnatinsa.