-
Takunkumi Bai Hana Shigar Da Makamai A Sudan Ta Kudu Ba
Nov 29, 2018 06:34Kungiyar (Conflict Armament Research) ta Birtaniya, ta fitar da wani rahoto wanda ke cewa takunkumin da aka kakaba wa Sudan ta Kudu kan makaman yaki bai yi wani tasiri ba.
-
Madagaska : Kotun Tsarin Mulki Ta Amince Da Sakamakon Zabe Zagaye Na farko
Nov 29, 2018 05:39Kotun tsarin mulki a Madagaska, ta yi na'am da sakamakon zaben shugaban kasar zagaye na farko, da hukumar zaben kasar (CENI), ta sanar yau kusa da mako biyu.
-
Congo:Amurka Ta Rufe Ofishin Jakadancinta Kwanaki 4 A Jere
Nov 29, 2018 03:23Kamfanin dillancin Labarun Faransa ya ce; An shiga kwana na 4 da Amurkan ta rufe ayyukan ofishin jakadancinta da yake a birnin kinshasha na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
-
Buhari Ya Sha Alwashin Goyon Bayan Sojojin Nijeriya Har Sai Sun Cimma Manufarsu
Nov 28, 2018 14:00Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya bayyana cewar gwamnatinsa ta kuduri aniyar kara karfafa sojojin kasar a ci gaba da fada da ta'addanci da suke yi a yankin Arewa maso Gabashin kasar, yana mai cewa gwamnatin tasa za ta yi dukkanin abin da za ta iya wajen goyon bayan sojojin don cimma abin da suka sa gaba a yankin.
-
Wata 'Yar Kunar Bakin Wake Ta Raunana Mutane 29 A Kasar Kamaru
Nov 28, 2018 13:59Jami'an tsaron kasar Kamaru sun tabbatar da samun raunin mutane 29 sakamakon wani harin kunar bakin wake da wata mace ta kai a yau din nan Laraba a garin Amchide da ke yanki arewa mai nisa na kasar.
-
CAF: Issa Hayatou Zai Biya Diyya Ta Yuro Miliyan 24,5
Nov 28, 2018 02:25Kotun tattalin arziki ta birnin Alkahira na Masar, ta yanke hukuncin biyan diyya ta Miliyan 24,5 ga tsahon shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika, Issa Hayatou, saboda sanya hannu kan wata kwangila ta 'yancin kafofin sadarwa dana kasuwancin harkar kwallon Afrika da wani kamfani mai Lagardère Sports na Faransa.
-
Nijar : An Rufe Cibiyoyin Biritaniya Da Ke Zubar Da Ciki
Nov 28, 2018 01:56Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayar da umarnin dakatar da aikin wasu cibiyoyi biyu na wata kungiyar agajin kasa da kasa ta Birtaniya, mai suna (Marie Stopes International), bisa zargin ayyukan zubar da ciki ba bisa ka'ida ba.
-
Gabon: Ali Bongo Zai Bar Saudiyya, Don Ci Gaba Da Jinya A Morocco
Nov 28, 2018 00:02A wani lokaci yau Laraba ne ake sa ran shugaba Ali Bongo na Gabon zai fice daga Saudiyya, domin ci gaba da jinya a kasar Morocco.
-
Sojojin Saman Nijeriya Sun Yi Luguden Wuta Kan Sansanin Boko Haram A Yankin Tekun Chadi
Nov 27, 2018 14:24Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta kaddamar da wasu hare-hare ta sama a wasu yankuna na Tekun Chadi da aka ce sansanoni ne na 'yan kungiyar Boko Haram a ci gaba da mayar da martani ga harin ta'addancin da 'yan kungiyar suka kai wani sansanin sojin Nijeriya da yayi sanadiyyar mutuwar sama da sojoji 100.
-
Kasashen Afirka Sun Jaddada Muhimmanci Aiki Tare Wajen Fada Da Ta'addanci
Nov 27, 2018 14:23Kasashe mahalarta taron kasa da kasa kan fada da ta'addanci da aka gudanar a kasar Aljeriya sun jaddada wajibcin aikin tare musamman a tsakanin kasashen Yammacin Afirka a matsayin babban abin da zai kawo nasara a fadar da ake da ta'addanci.