Nijar : An Rufe Cibiyoyin Biritaniya Da Ke Zubar Da Ciki
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayar da umarnin dakatar da aikin wasu cibiyoyi biyu na wata kungiyar agajin kasa da kasa ta Birtaniya, mai suna (Marie Stopes International), bisa zargin ayyukan zubar da ciki ba bisa ka'ida ba.
Wata sanarwa da ma'aikatar kiwan lafiya ta kasar ta fitar ta ce an dau matakin ne bayan wani bincike da sashen kwararu na ma'aikatar ya gudanar a cibiyar ta tsara iyalin ta Marie Stopes International a Yamai babban birnin kasar, inda aka gano ta'asar da wannan kungiyar ke aikatawa.
Sanarwar ta ce wannan ya saba wa ayar doka mai lamba 2006 ta 16 zuwa 21 kan tsarin lafiyar iyali, wanda ya tanadin zubar da ciki, har sai in hakan yana barazana ga rayuwar mace, sakamakon cikin da take dauke da shi.
Matakin dai ya shafi cibiyoyin kungiyar dake birnin Yamai da kuma jihar Maradi.
Ko a kwanan baya ma dai gwamnatin Kenya ta dauki irin wannan matakin, na dakatar da aikin wannan kungiyar.