Congo:Amurka Ta Rufe Ofishin Jakadancinta Kwanaki 4 A Jere
Nov 29, 2018 03:23 UTC
Kamfanin dillancin Labarun Faransa ya ce; An shiga kwana na 4 da Amurkan ta rufe ayyukan ofishin jakadancinta da yake a birnin kinshasha na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
Tun a ranar 29 ga watan Nuwamba da ake ciki ne dai Amurkan ta sanar da cewa; Ta sami bayanai kwarara da suke nuni da cewa za a kai wa gine-ginen Amurka harin ta'addanci.
A bisa wancan rahoton ne ta dakatar da ayyukan ofishin jakadancin har sai illa masha Allahu.
Wannan matakin na Amurka ya zo ne a daidai lokacin da kasar ta Demokradiyyar Congo take shirin gudanar da manyan zabuka a ranar 23 ga watan Disamba
Babu wani bayani da ya fito daga gwamnatin kasar ta Congo dangane da matakin na Amurka na rufe ofishin jakadancinta