Madagaska : Kotun Tsarin Mulki Ta Amince Da Sakamakon Zabe Zagaye Na farko
Nov 29, 2018 05:39 UTC
Kotun tsarin mulki a Madagaska, ta yi na'am da sakamakon zaben shugaban kasar zagaye na farko, da hukumar zaben kasar (CENI), ta sanar yau kusa da mako biyu.
Sakamakon zaben da hukumar ta CENI ta fitar da ya nuna dan takara Andry Rajoelina ne kan gaba da 39,23% a yayin da Marc Ravalomanana ya samu 35%.
Hakan ne ya bada damar zuwa zagaye na biyu a zaben shugaban kasar tsakanin 'yan takara Andry Rajoelina da Marc Ravalomanana.
A ranar 19 ga watan Disamba mai shirin kamawa ne za'a gudanar da zaben shugaban kasar ta Madagaska a zagaye na biyu, a yayin da za'a fara yakin neman zaben a ranar 4 ga watan na Disamba.
Tags