CAF: Issa Hayatou Zai Biya Diyya Ta Yuro Miliyan 24,5
(last modified Wed, 28 Nov 2018 05:55:12 GMT )
Nov 28, 2018 05:55 UTC
  • CAF: Issa Hayatou Zai Biya Diyya Ta Yuro Miliyan 24,5

Kotun tattalin arziki ta birnin Alkahira na Masar, ta yanke hukuncin biyan diyya ta Miliyan 24,5 ga tsahon shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika, Issa Hayatou, saboda sanya hannu kan wata kwangila ta 'yancin kafofin sadarwa dana kasuwancin harkar kwallon Afrika da wani kamfani mai Lagardère Sports na Faransa.

Hukuncin biyan diyyar dai ya shafi shi tsohon hukumar ta CAF, wato Issa Hayatou da kuma tsohon babbn sakatarensa dan asalin kasar Marocco, Hicham El Amrani.

Wannan hukuncin dai an zuwa ne shekara biyu bayan da hukumomin kasar Masar suka bankado hannun shi tsohon shugaban hukumar ta CAF dan asalin kasar Kamaru, da tsohon babban sakataren a badakalar data shafi kwangilar.

Babban laifin da ake tuhumarsu da shi, shi ne baiwa kamfanin na Faransa (LSE) a takaice damar tafiyar da harkokin sadarwa da kasuwanci na harkar kwallon Afrika a tsakanin shekara 2017-2028, kan kudi dalar Amurka Biliyan guda, wanda kuma yarjejeniyar ta sabawa doka a kasar ta Masar inda hukumar ta CAF ke da cibiyarta.