-
Uganda : Zaizayar Kasa Ta Yi Ajalin Mutum 7
Oct 11, 2018 15:35Mutane 7 ne aka tabbatar da mutuwarsu sanadiyyar zaizayar kasa wacce ta biyu bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya a yau Alhamis a kasar Uganda.
-
Najeriya : Obasanjo Ya Sasanta Da Atiku Abubakar
Oct 11, 2018 15:33Tsohon shugaban kasar tarayyar Najeria Olusegun Obasanjo ya sasanta da Atiku Abubakar, inda ya yafe masa duk laifuffukan da ya yi masa a baya ya kuma amince da cewa zai goyi bayansa a zabe na shekara ta 2019.
-
Ma'aikatan Filin Jirgin Sama A Lagos Sun Yi Barazanar Fadada Yajin Aikin
Oct 11, 2018 15:32Kungiyar ma'aikatan tashar jiragen sama ta Murtala Mohammad a birnin Lagos a Najeria ta yi barazanar fadada yajin aikin da take yi saboda korar wasu abokan aikinsu wanda hukuma mai kula da tashar jiragen saman ta yi.
-
Tashin Bom Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Sojoji 3 A Kasar Mali
Oct 11, 2018 15:30Sojojin Kasar Mali 3 ne suka rasa rayukansu a lokacinda motarsu ta taka nakiya a tsaikiyar kasar a daren jiya Laraba.
-
Boko Haram : An Kashe Sojojin Najeriya 7
Oct 11, 2018 08:50Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato wata sanarwa ta sojojin Najeriya da take cewa an kashe 7 daga cikinsu akan iyakar kasar da jamhuriyar Nijar.
-
AU Ta Bukaci 'Yan Siyasa A Kamaru Da Su Kai Zuciya Nesa
Oct 11, 2018 04:20Kungiyar tarayyar Afrika ta kirayi 'yan siyasa akasar Kamaru da su kai zuciya nesa, a lokacin da ake jiran sakamakon zaben da aka gudanar a kasar a makon da ya gabata.
-
Aljeriya Ta Ce Akwai Bukatar Garambawul A Tsarin Tafiyar Da Kungiyar Kasashen Larabawa
Oct 11, 2018 04:19Gwamnatin kasar Ajeriya ta bukaci da a yi wa tsarin tafiyar da kungiyar kasashen larabawa babban garambawul.
-
Uganda Zata Dauki Tsauraran Matakai Kan Kashe-Kashen Gilla
Oct 10, 2018 15:17Shugaban kasar Uganda ya bayyana cewa: Gwamnatinsa zata dauki tsauraran matakan shawo kan matsalolin tsaro da suke addabar kasar tare da hukunta masu hannu a gudanar da ayyukan ta'addanci a kasar.
-
Kungiyar Al-Shabab Ta Kashe Mutane 5 Kan Zargin Ayyukan Leken Asiri A Somaliya
Oct 10, 2018 15:16Kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab da ke kasar Somaliya ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane biyar bayan ta zarge su da gudanar da ayyukan leken asiri kan kungiyar.
-
Masar : An Zargi Tsohuwar Gwamnatin Mubarak Da Kashe-Kashen Gilla
Oct 10, 2018 15:16Dan tsohon shugaban Majalisar Dokokin Masar ya zargi tsohuwar gwamnatin kasar karkashin shugabancin Husni Mubarak da aiwatar da kashe-kashen gilla kan masu sabanin ra'ayi da ita.