Tashin Bom Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Sojoji 3 A Kasar Mali
Sojojin Kasar Mali 3 ne suka rasa rayukansu a lokacinda motarsu ta taka nakiya a tsaikiyar kasar a daren jiya Laraba.
Jaridar Punch ta Najeriya ta bayyana cewa majiyar sojojin kasar ta Mali ce ta bayyana haka a yau Alhamis ta kuma kara da cewa hatsarin ya auku ne tsakanin garin Koro da Jungani kusa da kan iyakar kasar da kasar Borki Faso. Sojoji ukku sun mutu a yayinda wasu hudu suka ji rauni.
Har'ila yau majiyar hukumomi a yankin ta tabbatar da labarin ta kuma kara da cewa irin wannan aiki na yan ta'adda ne da suke yankin.
Kasar Mali dai tana fama da tashe tashen hankula tun shekara ta 2012 a lokacinda buzaye daga arewacin kasar suka yi kokarin bellewa daga kasar, amma sai yan ta'adda masu kishin addini suka kwace lamura daga hannunsu suka kuma kwace iko da wurare da dama a yankin. Amma sojojin Faransa da kuma na MDD suka sake dawo da ikon gwamnati a yankin. Sai dai hakan bai hanasu kai hare-hare kan sajojin kasar daga lokaci zuwa lokaci ba.