Boko Haram : An Kashe Sojojin Najeriya 7
Oct 11, 2018 12:20 UTC
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato wata sanarwa ta sojojin Najeriya da take cewa an kashe 7 daga cikinsu akan iyakar kasar da jamhuriyar Nijar.
Bayanin ya ci gaba da cewa an kashe sojojin ne bayan taho mu gama da aka yi a tsakaninsu da 'yan kungiyar Boko Haram a jahar Borno da ke arewa maso gabacin kasar.
Sai dai sojojin na Najeriya sun kashe 'yan kungiyar ta Boko Haram da dama a yayin gumurzun.
Kungiyar ta Boko haram wacce take da alaka da Isis tana a matsayin babbar barazanar tsaro ga kasashen da suke a bakin tafkin Chadi.
Daga 2010 zuwa yanzu kungiyar ta kashe fiye da mutane 20,000 a cikin kasar ta Najeriya da kasashen makwabta.
Tags