Najeriya : Obasanjo Ya Sasanta Da Atiku Abubakar
Tsohon shugaban kasar tarayyar Najeria Olusegun Obasanjo ya sasanta da Atiku Abubakar, inda ya yafe masa duk laifuffukan da ya yi masa a baya ya kuma amince da cewa zai goyi bayansa a zabe na shekara ta 2019.
Jaridar Premiumtimes ta Najeriya ta bayyana cewa Alhaji Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar Jam'iyyar PDP ya kai ziyara tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar zuwa gidan Obasanjo a Abeokuta a yau Alhamis, inda tsohon shugaban kasar ya tabbatar da cewa ya yafewa Atiku kura-kurai na baya ya kuma amince da goya masa baya a zaben shekara mai zuwa. Obasanjo ya ce ya tabbatar da cewa Atiku ya gyara halinsa don haka yana goyon bayansa a zaben shekara mai zuwa.
Kafin haka dai Atiku Abubakar, shi ne mataimakin shugaban kasa a lokacin shugabancin Obasanjo, kuma shi ne yakamata ya gaji shi bayan ya kammala wa'adinsa na shekaru 8 kan kujerar shugabancin kasar a shekara 2007, amma sabani a tsakaninsu ya hana hakan faruwa.