-
IRGC: Iran Za Ta Ci Gaba Da Kera Makamanta Ko Za'a Sa Mata Sabbin Takunkumi Kuwa
Mar 12, 2016 05:28Mataimakin babban hafsan hafsoshin dakarun kasar Iran Birgediya Janar Massoud Jaza'iri ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da shirinta na kera makamai masu linzami ko da kuwa hakan zai sa a sanya wata masu sabbin takunkumi ne.
-
Ayatullahi Imami Kashani: Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Abin Koyi Ne Ga Kasashen Duniya
Mar 11, 2016 13:41Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a babban Masallacin Juma'ar birnin Tehran na kasar Iran ya jaddada cewa; Makiya basu da karfin gwiwar daukan matakin wuce gona da iri kan kasar Iran sakamakon himman al'ummar kasar da shirin ko-ta kwanan dakarun Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
-
Jagora: Yakukuwan Da Ke Faruwa A Gabas Ta Tsakiya Na Siyasa Ne Kawai
Mar 10, 2016 14:18Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar yakukuwan da suke faruwa a Gabas ta tsakiya, wasu yakukuwa ne da suke da alaka da siyasa sannan kuma don cimma manufofi na siyasa, yana mai watsi da kokarin Amurka da sahyoniyawa na haifar da rarrabuwan kai tsakanin Shi'a da Sunna a yankin da ma duniya baki daya.
-
Norooz
Mar 08, 2016 09:06Sabuwar Shekarar Parsiawa Ta Bana
-
'Yan Majalisar Iran Sun Sake Jaddada Goyon Bayansu Ga Kungiyar Hizbullah
Mar 08, 2016 02:14Sama da 'yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran 200 ne suka nuna goyon bayansu ga kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon da kuma yin Allah wadai da matsayar da kungiyar larabawan Tekun Fasha na sanya kungiyar cikin kungiyoyin 'yan ta'adda.
-
Taron manema Labarai na shugaban kasar Iran
Mar 06, 2016 13:27Shugaban Rauhani:Dogoro kai ga Al'ummar Iran Shine gimshiki mai karfi na zaman tsarin Jumhoriyar musulinci a nan Iran
-
Ziyarar Firayi Ministan Turkiyya, Ahmet Davutoglu, Zuwa Iran
Mar 06, 2016 02:20A daren shekaran jiya Juma'a ne firayi ministan kasar Turkiyya Ahmet Davutoglu tare da wata babbar tawaga ta 'yan siyasa da 'yan kasuwa ya iso nan Tehran, inda a jiya Asabar ya gana da shugaban kasar Iran da mataimakinsa bugu da kari kan wasu manyan 'yan kasuwa na kasar.
-
Ziyarar Piraministan Kasar Turkiya A Iran
Mar 05, 2016 16:17Oglu: Cinikiyya Tsakanin Iran Da Turkiya Za ta kai Dala Biliyan 50
-
Allah Yayi Wa Ayatullah Tabasi, Mai Kula Da Haramin Imam Ridha, Rasuwa
Mar 04, 2016 13:25A safiyar yau Juma'a ne Allah Yayi wa Ayatullah Abbas Wa'iz Tabasi, wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a lardin Khorasan sannan kuma mai kula da haramin Imam Ridha (a.s) da ke birnin Mashhad, rasuwa bayan rashin lafiyar da yayi fama da shi.
-
Limamin Juma'ar Tehran Yayi Allah Wadai Da Sanya Hizbullah Cikin Kungiyoyin Ta'addanci Da Larabawa Suka Yi
Mar 04, 2016 12:25Na'aibin limamin Juma'ar birnin Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami yayi Allah wadai da sanya kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon cikin kungiyoyin ta'addanci da kungiyar kasashen larabawan Tekun Fasha ta yi, yana mai bayyana hakan a matsayin hadin baki da haramtacciyar kasar Isra'ila.