Allah Yayi Wa Ayatullah Tabasi, Mai Kula Da Haramin Imam Ridha, Rasuwa
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i1882-allah_yayi_wa_ayatullah_tabasi_mai_kula_da_haramin_imam_ridha_rasuwa
A safiyar yau Juma'a ne Allah Yayi wa Ayatullah Abbas Wa'iz Tabasi, wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a lardin Khorasan sannan kuma mai kula da haramin Imam Ridha (a.s) da ke birnin Mashhad, rasuwa bayan rashin lafiyar da yayi fama da shi.
(last modified 2018-08-22T06:57:55+00:00 )
Mar 04, 2016 13:25 UTC
  • Allah Yayi Wa Ayatullah Tabasi, Mai Kula Da Haramin Imam Ridha, Rasuwa

A safiyar yau Juma'a ne Allah Yayi wa Ayatullah Abbas Wa'iz Tabasi, wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a lardin Khorasan sannan kuma mai kula da haramin Imam Ridha (a.s) da ke birnin Mashhad, rasuwa bayan rashin lafiyar da yayi fama da shi.

Rahotanni daga birnin Mashhad din sun bayyana cewar a safiyar yau Juma'a ne Ayatullah Tabasi, dan shekaru 80 a duniya ya rasu a wani asibiti a birnin Mashad bayan kwantar da shi da aka yi a wajen na tsawon mako guda saboda matsalar numfashi da yake fama da ita.

Ayatullah Tabasi dai ya kasance daga cikin manyan malamai na kurkusa da marigayi Imam Khumaini (r.a), sannan kuma ya taka gagarumar rawar yayin juyin juya halin Musulunci da kuma bayan juyin. Ya kasance yana rike da wannan mukami na mai kula da haramin Imam Ridha (a.s) din ne tun farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci bayan da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya nada shi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, cikin wani sakon ta'aziyya da ya fitar ya bayyana marigayi a matsayin babban bawan Allah kana kuma mabiyin marigayi Imam Khumaini (r.a) na hakika.

A gobe Asabar ne ake sa ran za a yi jana'aizarsa a birnin na Mashhad inda ake sa ran manyan jami'an kasar ta Iran da kuma wasu daga wajen kasar za su halarta.