Taron manema Labarai na shugaban kasar Iran
Shugaban Rauhani:Dogoro kai ga Al'ummar Iran Shine gimshiki mai karfi na zaman tsarin Jumhoriyar musulinci a nan Iran
Yayin taron manema Labarai da ya gabatar a marecen yau, shugaban Jumhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rauhani ya yi ishara kan zaben 'yan Majalisun Dokoki da na kwararu da ya gudana a ranar 26 ga watan Favrayun da ya gabata, inda ya Al'ummar Iran sun sake bayyana dogaransu ga tsarin Jumhoriyar musulinci da kuma jagoran juyinm juya hali, kuma yadda milyoyin Al'ummar kasar suka fito a zaben ya sanya Duniya cikin ba zata.
Rauhani ya ce halartar da mafi yawan 'yan kasar suka yi a zaben 'yan Majalisun dokoki da na kwararu ya kara karfafa tsarin musulci fiye da baya, kuma Gwamnati ta yi iya kokarinta wajen gudanar da zaben cikin sauki ga Al'umma.
Yayin da yake ishara kan yanayi tsaro a yayin zaben, Shugaban Jumhoriyar musulinci na Iran ya bayyana cewa bisa kokarin dukkanin ma'aikatun tsaro da bangarorin siyasar kasar, zaben ya gudanar cikin cikekken tsaro da konciyar hankali.
Har ila yau Shugaba Rauhani ya tabbatar da cewa dukkanin mahukuntan kasar na aiki tare domin ci gaban Al'ummar Iran babu wata majalisa da za a ce tana bayan Gwamnati ko kuma tana adawa da ita, dukkanin bangarorin na aiki tare domin ci gaban kasa.
Yayin da yake ishara kan batun dake takunkumin da aka kakabawa kasar, Shugaba Rauhani ya ce kafin cimma wannan yarjejjeniya wasu kasashe na da'awar cewa kasar Iran babbar barazana ce ga harakokin tsaron Duniya, amma a yau kasar ta koma muhimiyar kasa a tsakanin kasashen Duniya