Ziyarar Piraministan Kasar Turkiya A Iran
Oglu: Cinikiyya Tsakanin Iran Da Turkiya Za ta kai Dala Biliyan 50
Pira minisan kasar Turkiya Dau'du Oglu ya ce; alaka a tsakanin Turkiya da Iran ta bude wani sabon shafi na bunkasa bayan cire takunkumi.
Ahmad Dauu Oglu wanda ya ke jawabi a wurin taron kwamitin kasuwan na Iran da Turkiya, ya ce ganawar da ya yi da mahukuntan Iran ta yi amfani sannan kuma ya kara da cewa; Abinda mu ke so, shi ne Turkiya da Iran su zama tamkar dan juma da dan jummai, kuma matukar akwai manufa ta siyasa to abu ne mai yiyuwa.
Pira ministan na Turkiya ya kara da cewa; bagiren da su ke a ciki da makwabtaka da juna, sun maida Turkiya ta zama kofar Iran ta shiga turai, ita kuma Iran ta zamarwa Turkiya kofar shiga Asiya.
Oglu ya kuma ce ya kamata cinikayya a tsakanin kasashen biyu ya kamata ta haura dalar Amurka biliyan 30, domin ta kai dalar biliyan 50.