-
Jagora: Ficewar Amurka Daga Yarjejeniyar Nukiliya Bai Zo Mana A Matsayin Ba Za Ta Ba
May 09, 2018 06:13Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar sanarwar ficewa daga yarjejeniyar nukiliya da shugaban Amurka yayi a daren jiya bai zo masa a matsayin wani abin mamaki ba, yana mai cewa al'ummar Iran za su ci gaba da riko da tafarkin da suke kai ba tare da tsoron wani ba.
-
'Yan Majalisar Iran Sun Gabatar Da Kuduri Kan Ficewar Amurka Daga Yarjejeniyar Nukiliya
May 09, 2018 06:12'Yan majalisar shawarar Musulunci ta Iran sun yi Allah wadai da sanarwar da shugaban Amurka yayi na ficewa daga yarjejeniyar nukiliyan kasar Iran suna masu gabatar da wani daftarin kuduri ga gwamnatin kasar kan yadda za a mayar wa Amurka da martani kan hakan.
-
Rouhani Ya Mayar Da Martani Ga Ficewar Amurka Daga Yarjejeniyar Nukiliya
May 09, 2018 06:11Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar Iran za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliya duk kuwa da ficewar Amurka daga cikinta amma da sharadin sauran kasashen Turai za su ci gaba da girmama ta sannan kuma Iran za ta cimma abin da ta ke so.
-
Amurka Ta Fice Daga Yerjejeniyar Shirin Nukliyar Kasar Iran
May 08, 2018 14:35Shugaban kasar Amurka Donald Trump Ya Bayyana Ficewar Kasar Amurka daga yerjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran wacee kasar ta Amurka da wasu manya manyan kasashen duniya 5 suka kulla tare da kasar ta Iran a shekara ta 2015.
-
Janar Baqeri: Babu Wata Kasar Da Ta Isa Ta Yi Wa Iran Barazana
May 08, 2018 06:43Babban hafsan hafsoshin dakarun kasar Iran, Manjo Janar Muhammad Baqeri ya ja kunnen makiyan Iran da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da kakkausar martani kan duk wani wuce gona da iri da makiyan za su yi a kan kasar Iran.
-
Rasha: Wajibi Ne A Kare Yarjejeniyar Nukiliyar Iran
May 07, 2018 14:27Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergey Ryabkov ne ya bayyana haka a yau litinin sannan ya kara da cewa; Rasha tana son ganin dukkanin bangarorin yarjejeniyar sun ci gaba da aiki da ita
-
Qassemi: Amurka Za Ta Yi Nadamar Ficewa Daga Yarjejeniyar Nukiliya
May 07, 2018 06:41Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran, Bahram Qassemi, ya bayyana cewar Amurka za ta yi nadama mai girma matukar ta fice daga yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da Iran.
-
Jami'an Tsaron Iran Sun Kama Wani Dan Ta'adda Da Ke Son Kai Hari Birnin Mashad
May 06, 2018 06:49Jami'an tsaron kasar Iran sun sanar da kama wani mutum da ke da alaka da kungiyar ta'addancin nan ta munafukai MKO wanda yake kokarin kai wasu hare-haren ta'addanci a birnin Mashad mai tsarki.
-
Rouhani: Bakin Al'ummar Iran Ya Zo Daya Kan Trump Da HK.Isra'ila
May 06, 2018 06:48Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewa bakin al'ummar Iran ya zo daya dangane da shugaban Amurka da H.K.Isra'ila, yana mai jan kunnen Amurka dangane da batun ficewa daga yarjejeniyar nukiliya yana mai cewa Iran tana da hanyoyin kare kanta daga duk wata barazana.
-
Na'ibin Limamin Jumma'a A Tehran Ya Ce Barazanar Amurka Ba Zata Girgiza Iran Ba
May 04, 2018 14:31Limamin da ya jagoranci sallar Jumma'a a nan tehran ya bayyana cewa barazanar Amurka da kawayenta na yankin gabas ta tsakiya ba za ta girgiza kasar Iran ba.