Amurka Ta Fice Daga Yerjejeniyar Shirin Nukliyar Kasar Iran
Shugaban kasar Amurka Donald Trump Ya Bayyana Ficewar Kasar Amurka daga yerjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran wacee kasar ta Amurka da wasu manya manyan kasashen duniya 5 suka kulla tare da kasar ta Iran a shekara ta 2015.
Shugaban Amurka ya bayyana wannan matsayin ne a wani jawabin da ya gabatar a dazo-dazun nan a fadar white house. amma shugaba majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali shamkhani ya bayyana cewa Amurka ce zata fara cutuwa da kurakuranta.
Shamkhani ya bayyana haka ne a yau Talata a dai-dai lokacinda ake jiran matsayin da shugaban kasar Amurka Donald Trump zai dauka dangane da yerjejeniyar a yau.
Ali Shamkhani ya kara da cewa, babban kuskuren da kasashen turai zasu yi idan shugaban kasar Iran ya fice daga wannan yerjejeniyar shi ne nuna goyon bayansu ga matakan da zai dauka, amma ba zai dade ba Amurka zata dawo daga rikiyarsu.
Shugaban majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya kara jaddada cewa kasar Iran ba zata taba amincewa da sake tattaunawa kan shirinta na makamashin Nukliya ba, bayan da Amurka ta fice daga yerjejeniyar, sannan a shirye take ta fuskanci duk wani matakin da zata dauka a kanta kan shirin nata.
Da misalin karfe 10.30 na daren yau ne shugaban kasar Amurka ya bayyana ficewar kasarsa daga yerjejeniyar.