-
Zarif: Iran Na Da Hakkin Mayar Da Martani Idan Amurka Ta Fice Daga Yarjejeniyar Nukiliya
May 03, 2018 12:54Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da hakkin mayar da martani matukar dai Amurka, a matsayinta na wani bangare na yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma a shekara ta 2015, ta fice daga cikinta.
-
Iran Ta Musunta Zargin Marocco Na Taimaka Wa Polisario
May 03, 2018 00:52Jamhuriya Musulinci ta Iran ta yi fatali da zargin Marocco na cewa tana taimaka wa kungiyar 'yan Polisariyo ta yammacin Sahara.
-
Iran Ta Mayar Da Martani Ga Kalaman Netanyahu Kan Shirin Nukiliyanta
May 01, 2018 00:58Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran, Bahram Qassemi, yayi watsi da tuhumce-tuhumcen da firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu yayi kan Iran yana mai cewa babu wani abin da ke cikin kalaman Netanyahun in ban zuki ta malle da kuma kokarin maras fa'ida.
-
Rauhani Da Macron Sun Tattauna Batun Yarjejeniyar Shirin Iran Na Nukiliya
Apr 30, 2018 02:16Shugabannin kasashen Iran da Faransa sun tattauna ta wayar tarho kan muhimman batutuwa da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma batun yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya.
-
Kwamandan Sojojin Iran: Kasashen Turai Sun Fada Tarkon Yaudarar Amurka
Apr 29, 2018 01:12Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Sayyid Abdulrahim Musawi ya bayyana cewar gwamnatocin 'yan mulkin mallaka karkashin jagorancin Amurka suna fada ne da juyin juya halin Musulunci na Iran, yana mai cewa a halin yanzu kasashen Turai sun fada tarkon yaudarar Amurka.
-
An Shiga Rana Ta Biyu A Gasar Kur'ani Ta Duniya Ta Daliban Jami'a Musulmi A Mashhad
Apr 28, 2018 13:13A yau ne aka shiga rana ta biyu a ci gaba da gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani ta duniya wadda ta kebanci daliban jami'a musulmi, wadda ake gudanarwa a birnin Mashhad na kasar Iran.
-
Shugaba Rauhani Ya Taya Al'ummar Saliyo Murnar Zagayowar Ranar Samun 'Yancin Kasar
Apr 28, 2018 13:09Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya taya al'ummar kasar Saliyo murnar zagayowar lokacin samun 'yancin kankasar.
-
Na'ibin Limamin Juma'ar Tehran: Shekaru 40 Kenan Al'ummar Iran Suke Tinkarar Ma'abota Girman Kai
Apr 27, 2018 11:37Wanda ya jagoranci sallar Juma'ar birnin Tehran ya bayyana cewar shekaru 40 kenan al'ummar Iran suka tsaya kyam wajen tinkarar girman kai da son mulkin mallakar Amurka, kuma a nan gaba ma za su ci gaba da yin hakan.
-
Iran : Jagora Ya Yi Kira Ga Hadin Kan Musulmi
Apr 26, 2018 23:06Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya yi kira ga wajabcin hadin kan musulmi, a daidai lokacin da a cewarsa manyan kasashen duniya ke kara shishigi a harkokin kasashe, ta hanyar keta huriminsu.
-
Jagora: Iran Ta Tsaya Kyam Kan Fin Karfin Makiya
Apr 26, 2018 07:25Jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyid Aliyul Khamina'i ya bayyana cewa JMI ta tsaya kyem kan fin karfin da kasashen masu girman kai suke son yi mata kimani shekaru 40 a halin yanzu, godiya ga karantarwar Al-Qur'ani mai girma.