Iran Ta Musunta Zargin Marocco Na Taimaka Wa Polisario
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i30500-iran_ta_musunta_zargin_marocco_na_taimaka_wa_polisario
Jamhuriya Musulinci ta Iran ta yi fatali da zargin Marocco na cewa tana taimaka wa kungiyar 'yan Polisariyo ta yammacin Sahara.
(last modified 2018-08-22T11:31:47+00:00 )
May 03, 2018 05:22 UTC
  • Iran Ta Musunta Zargin Marocco Na Taimaka Wa Polisario

Jamhuriya Musulinci ta Iran ta yi fatali da zargin Marocco na cewa tana taimaka wa kungiyar 'yan Polisariyo ta yammacin Sahara.

Gwamnatin ta Moroko dai ta tuhumi Iran da cewa tana taimakawa kungiyar yammacin Sahara ta Polisariyon, ta hanyar kungiyar Hezbollah ta Labanon don haka ta sanar da yanke huldar diplomasiyya da Iran din a ranar Talata.

Da yake maida martani kan matakin, ministan harkokin wajen Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya ce wannan zargin bai da tushe balle makama, tare da cewa Jamhuriya Musulinci ta Iran a koda yaushe na mutunta hurimi da tsaron kasashen da take da huldar diflomatsiyya dasu, hasali ma bata tsoma baki a harkokinsu.

Kasar Saudiyya wacce ke cacar baki da Iran, ta yaba da matakin na Marocco, a yayin da kungiyar Hezbollah da ta 'yan Polisariyo da kuma kasar Aljeriya suka yi fatali da zargin na Marocco da suka danganta da marar tushe.