Kwamandan Sojojin Iran: Kasashen Turai Sun Fada Tarkon Yaudarar Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i30386-kwamandan_sojojin_iran_kasashen_turai_sun_fada_tarkon_yaudarar_amurka
Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Sayyid Abdulrahim Musawi ya bayyana cewar gwamnatocin 'yan mulkin mallaka karkashin jagorancin Amurka suna fada ne da juyin juya halin Musulunci na Iran, yana mai cewa a halin yanzu kasashen Turai sun fada tarkon yaudarar Amurka.
(last modified 2018-08-22T07:01:46+00:00 )
Apr 29, 2018 01:12 UTC
  • Kwamandan Sojojin Iran: Kasashen Turai Sun Fada Tarkon Yaudarar Amurka

Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Sayyid Abdulrahim Musawi ya bayyana cewar gwamnatocin 'yan mulkin mallaka karkashin jagorancin Amurka suna fada ne da juyin juya halin Musulunci na Iran, yana mai cewa a halin yanzu kasashen Turai sun fada tarkon yaudarar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran Hukumar Gidan Radiyo da Talabijin na Iran ya bayyana cewar Manjo Janar Abdulrahim Musawi ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai inda yayin da yake mayar da martani dangane da kalaman wasu jami'an kasashen Turai na baya-bayan dangane da karfin kariya da Iran take da shi ya bayyana cewar: Ma'abota girman kan duniya karkashin jagorancin Amurka suna adawa ne da juyin juya halin Musulunci na Iran sannan wasu kasashen Turai kuma ido rufe son fada tarkon yaudarar Amurka.

Janar Musawi ya bayyana irin yadda ma'abota girman kan suke yi ta magana kan shirin nukiliyan Iran da tattaunawa kansa, wata rana din kuma su taso da maganar take hakkokin bil'adama a Iran da kuma yadda a halin yanzu suke ta magana kan batun irin karfin kariya da Iran take da shi a matsayin alamu na irin wannan adawa da suke yi da Iran.

Kwamandan sojojin na  Iran ya jaddada shirin da dakarun kasar suke da shi na kare kasar daga duk wata barazana da makiya za su iya yi mata