Iran Ta Mayar Da Martani Ga Kalaman Netanyahu Kan Shirin Nukiliyanta
Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran, Bahram Qassemi, yayi watsi da tuhumce-tuhumcen da firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu yayi kan Iran yana mai cewa babu wani abin da ke cikin kalaman Netanyahun in ban zuki ta malle da kuma kokarin maras fa'ida.
Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya bayyana hakan ne a safiyar yau Talata inda ya ce shugabannin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kware wajen amfani da barazana da kararraki wajen kiyaye haramtacciyar kasarsu, yana mai cewa ya kamata Netanyahu da haramtacciyar gwamnatinsu mai kashe kananan yara ta sahyoniyawa sun san cewa a halin yanzu dai al'ummomin duniya suna sane da abubuwan da ke gudana.
Kafin hakan ma dai ministan harkokin wajen na Iran, Dakta Muhammad Jawad Zarif, cikin wani sako da ya rubuta a shafinsa na Twitter, yayi watsi da wadannan kalaman na Netanyahu yana mai bayyana shi a matsayin karamin yaro da ba zai iya hana aiwatar da wani abu ba.
A daren jiya ne dai firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ilan ya gabatar da wani jawabi da 'yan wasu hotuna a matsayin abin da ya kira hujjojin da ke tabbatar da cewa Iran ta yi karya wa dangane da shirinta na nukiliya wanda ya kira shi a matsayin wani shiri na kera makaman nukiliya.