Jagora: Iran Ta Tsaya Kyam Kan Fin Karfin Makiya
Jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyid Aliyul Khamina'i ya bayyana cewa JMI ta tsaya kyem kan fin karfin da kasashen masu girman kai suke son yi mata kimani shekaru 40 a halin yanzu, godiya ga karantarwar Al-Qur'ani mai girma.
Tashar talabijon ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Jagoran ya fadi haka ne a yau Alhamis a lokacin da yake ganawa da mahaddatan Al-qur'ani mai girma wadanda suka halarci gasar karatun Al-qur'ani karu na 35 a nan Tehran.
Jagoran ya kara da cewa yakamata al-ummar musulmi su fahinci karatun an-qur'ani mai girma su kuma aiwatar da shi bayan haddarsa. Hanya daya tilo ta daukkakar musulmi a duniya ita ce aiwatar da shiriyar Allah da ke cikin al-qur'ani mai girma Inji jagoran.
Daga karshe jagoran ya bada misali da zancen shugaban kasar Amurka na baya bayan nan, kan cewa wasu kasashen gabas ta tsakiya ba za su wanzu na tsawon mako guda ba, in ba tare da taimakon Amurka ba, wannan na daga cikin illolin nisantar karantarwan Alqur'ani mai girma, wanda wasu kasashen musulmi suka yi.