Rauhani Da Macron Sun Tattauna Batun Yarjejeniyar Shirin Iran Na Nukiliya
(last modified Mon, 30 Apr 2018 06:46:59 GMT )
Apr 30, 2018 06:46 UTC
  • Rauhani Da Macron Sun Tattauna Batun Yarjejeniyar Shirin Iran Na Nukiliya

Shugabannin kasashen Iran da Faransa sun tattauna ta wayar tarho kan muhimman batutuwa da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma batun yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, a zanatawar da suka yi a daren jiya ta wayar tarho, shugaban kasar Iran Hassan Rauhani da kuma takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, sun jaddada wajabcin yin aiki da dukkanin abubuwan da yarjejeniyar nukiliya kan shirin Iran ta kunsa, wanda kuma hakan ya rataya ne a kan dukkanin bangarorin da suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar.

Dangane da alakar da tsakanin kasashen biyu kuwa, Rauhani da Macron sun tattauna kan hanyoyi kara bunkasa alaka ta kasuwanci da tattalin arziki a tsakanin Iran da Faransa, kasantuwar dukkanin kasashen biyu suna da bukatar juna juna a wasu bangarorin.