-
Britaniya Ta Ce Tana Tattaunawa Da Kawayenta Kan Sabbin Matakan Da Zasu Dauka Kan Iran
Apr 25, 2018 14:36Gwamnatin kasar Britaniya ta bayyana cewa tana tattaunawa da kawayenta don ganin irin matakan da zasu dauda kan Iran dangane da matsalolin da take haddasawa a yankin gabas ta tsakiya.
-
Iran Ta Samu Nasarar Tarwatsa Kungiyoyin 'Yan Ta'adda Sama Da 300 A Shekarar Bara
Apr 25, 2018 00:57Ministan tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri na Iran ya bayyana cewar a shekarar bara ta 1396 Hijira Shamsiyya, jami'an tsaron kasar sun sami nasarar tarwatsa kungiyoyin 'yan ta'adda sama da 300 da suke nufin aiwatar da hare-haren ta'addanci a kasar.
-
Zarif: Matukar Amurka Ta Fice Daga Yarjejeniyar Nukiliya, Iran Ba Za Ta Girmama Yarjejeniyar Ba
Apr 25, 2018 00:56Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar matukar dai Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da ita, to kuwa Iran ba ta ganin ya zama wajibi a kanta ta ci gaba da girmama yarjejeniyar, sannan kuma za ta dawo tace sinadarin uranium din da take yi a baya.
-
Iran Ta Yi Allawadai Da Harin Da Aka Kai Afganistan
Apr 23, 2018 06:40Jamhuriya Musulinci ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajenta, Bahram Qasemi, ta yi allawadai da kakkausar murya da harin kunar bakin waken da aka kai a Kabul, babban birnin kasar Afganistan a jiya Lahadi.
-
Yarjejeniyar Nukiliya : Iran Za Ta Dawo Da Shirinta Na Nukiliya, Idan Amurka Ta Janye
Apr 22, 2018 06:46Ministan harkokin wajen Jamhuriya Musulinci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta koma kan shirinta na nukiliya, idan har Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da ita.
-
Qasemi: Rahoton Amurka Kan Kare Hakkokin Bil Adama Batu Ne Na Siyasa
Apr 22, 2018 02:13Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya bayyana rahoton da Amurka ta fitar kan kare hakkokin bil adama a Iran da cewa magana ce ta siyasa kawai.
-
Kwamanda Fadavi: Matukar Gigi Ya Debi Makiya, To Za Su Fuskancin Fushin Dakarun IRGC Na Iran
Apr 21, 2018 01:14Kwamandan sojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran, Naval Commodore Ali Fadavi ya jaddda shirin da dakarunsa suke da shi na fada da duk wani nau'i na barazana ga tsaron Iran yana mai cewa matukar gigi ya debi makiyan, to kuwa za su fuskanci hakikanin fushin dakarun kare juyin.
-
Sheikh Siddiqi: Harin Da Aka Kaiwa Syria Alama Ce Ta Dabbanci A Cikin Lamarin Amurka
Apr 20, 2018 14:21Wanda ya jagoranci sallar Juma'a a Tehran ya bayyana cewa, harin da Amurka ta jagoranci wasu suka kaddamar a kan Syria, wata babbar alama ce kan yadda Amurka take yin watsi da dokokin kasa da kasa, tare da yin gaban kanta wajen aiwatar da siyasarta ta ina da yaki a duniya.
-
Limanin Juma'a Na Zanjan: Amurka Ba Za Ci Moriyar Yake-Yakenta A Gabas Ta Tsakiya Ba.
Apr 20, 2018 07:26Hijjatul Islam Ali Khatami Ya ce; Ko mai yawan kudaden da Amurka za ta kashe a yake-yaken da take yi a gabas ta tsakiya, ba zai haifar ma ta da mai ido ba.
-
Iran : Jagora Ya Daina Amfani Da Manhajar Telegram
Apr 18, 2018 13:30Shafin intarnet na adano da yada manufofin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya sanar da cewa Jagoran ya daina amfani da manhajar ''Telegram'' domin yin aiki da manhajojin sadarwa na zamani mallakin Iran, a matsayin martaba kasar.