Qasemi: Rahoton Amurka Kan Kare Hakkokin Bil Adama Batu Ne Na Siyasa
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya bayyana rahoton da Amurka ta fitar kan kare hakkokin bil adama a Iran da cewa magana ce ta siyasa kawai.
Kamfanin dillancin labaran Mehr ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake mayar da martani kan rahoton Amurka dangane da kare hakkin bil adama a Iran, Qasemi ya bayyana cewa Amurka bai kamata ta yi magana kan kare hakkin bil adama dangane da wasu kasashe ba, domin kuwa ita ce kasa ta farko a duniya wajen cin zarafin bil adama, da haifar da yake-yake da kisan dan adam a bayan kasa.
Ya ce maimakon bata lokaci da Amurka take yi domin cimma wasu manufofi na siyasa ta hanyar tuhumar wasu kasashe da take hakkin 'yan adam, da kamata ya yi ta fara da kare hakkokin bil adama a cikin kasarta, ta daina haifar da rikice-rikice a kasashen duniya, kuma ta daina mara baya ga Isra'ila kan kisan kiyashin da take yi wa Palastinawa kullum rana ta Allah.
Qasemi ya kara da cewa Amurka ta rasa abin da za ta tuhumi Iran da shi, illa batutuwa da suka shafi al'adu da addini, inda Amurka take kallon bata tarbiya da lalacewar dabi'a a matsayin hakkokin 'yan adam, wanda hakan a wurin al'ummar Iran ya sabawa addini da al'adarsu.