Apr 25, 2018 19:06 UTC
  • Britaniya Ta Ce Tana Tattaunawa Da Kawayenta Kan Sabbin Matakan Da Zasu Dauka Kan Iran

Gwamnatin kasar Britaniya ta bayyana cewa tana tattaunawa da kawayenta don ganin irin matakan da zasu dauda kan Iran dangane da matsalolin da take haddasawa a yankin gabas ta tsakiya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mai magana da yawun Theresa May yana fadar haka a yau Laraba, ya kuma kara da cewa kasashen suna duba yiyuwan amincewa da shawarar shugaban kasar Faransa na sake sabon tattaunawa kan shirin nukliyar kasar Iran wacce a wannan karon zata hada har da makamanta masu linzami.

A halin yanzu dai shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yana ziyarar aiki a kasar Amurka inda ya bukaci shugaban na Amurka kada ya fice daga yerjejeniyar shirin makamashin nukliya da kasar Iran ta shekara ta 2016. 

Shugaba Donald Trump dai ya bada lokaci zuwa ranarn 12 ga watan Mayu mai zuwa , ko kasashen da suka kulla  yerjejeniyar su amince a sake kulla wata sabuwar yerjejeniya ko kuma Amurka ta fice daga yerjejeniyar.

Gwamnatin kasar Iran dai ta bayyana cewa ba za ta sake shiga tattaunawa kan shirinta na makamashin nukliya da wata kasa ba, kuma ba za ta bude kofa don tattauna kan shirinta na makamai masu linzami ba. 

 

Tags