Iran : Jagora Ya Daina Amfani Da Manhajar Telegram
(last modified Wed, 18 Apr 2018 18:00:54 GMT )
Apr 18, 2018 18:00 UTC
  • Iran : Jagora Ya Daina Amfani Da Manhajar Telegram

Shafin intarnet na adano da yada manufofin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya sanar da cewa Jagoran ya daina amfani da manhajar ''Telegram'' domin yin aiki da manhajojin sadarwa na zamani mallakin Iran, a matsayin martaba kasar.

Sanarwar da aka wallafa kafin rufe hanyar sadarwa ta Telegram na Jagora, ta ce ta kira masu bibiyar shafin dasu koma kan manhajojin Iran, irinsu ''Soroush da Gap'' da hukumomin kasar ke da gurin ganin sun samu karbuwa.

Tuni dai wasu manyan jami'an kasar suka bi sahun jagoran wajen sanar da daina aiki da manhajar ta Telegram, inda mataimakin shugaban kasar Eshagh Jahangiri, da kuma kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Bahram Ghassemi, suka bi sahu ta hanyar rufe adireshinsu na Telegram. 

A daya bangere kuma ofishin shugaban kasar Hassan Rohani, ya fitar da wata sanarwa da haramta wa duk ma'aikatun gwamnati da na mallakin kasar aiki da wasu manhajoji sadarwa na kasashen ketare, a cewar kamfanin dilancin labaren Irna.

Ko a ranar Lahadi data gabata ministan ilimi na kasar, ya haramta wa dukkan makarantu yin aiki da manhajojin na kasashen waje, tare da umurtarsu su aiki da manhajoji na cikin gida.