Iran Ta Yi Allawadai Da Harin Da Aka Kai Afganistan
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i30212-iran_ta_yi_allawadai_da_harin_da_aka_kai_afganistan
Jamhuriya Musulinci ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajenta, Bahram Qasemi, ta yi allawadai da kakkausar murya da harin kunar bakin waken da aka kai a Kabul, babban birnin kasar Afganistan a jiya Lahadi.
(last modified 2018-08-22T11:31:44+00:00 )
Apr 23, 2018 11:10 UTC
  • Iran Ta Yi Allawadai Da Harin Da Aka Kai Afganistan

Jamhuriya Musulinci ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajenta, Bahram Qasemi, ta yi allawadai da kakkausar murya da harin kunar bakin waken da aka kai a Kabul, babban birnin kasar Afganistan a jiya Lahadi.

A yayin da yake jajanta wa al'umma da gwamnatin ta Afganistan, Mista Qasemi, ya danganta harin da rashin imani.

kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran din, ya yi fatan ganin an murkushe ta'addanci a wannan kasa ta Afganistan, kuma acewasa hakan ba zata samu ba sai kasashen yankin dana duniya sun hada karfinsu waje guda.

Harin na jiya Lahadi da aka kai kan wata cibiyar rejistar zabe a unguwar Hazara, ya dai yi sanadin mutuwar mutane a kalla hamsin da raunana wasu sama da 100, kuma kungiyar 'yan ta'adda ta IS ce ta dauki alhakin kai harin.