Rouhani Ya Mayar Da Martani Ga Ficewar Amurka Daga Yarjejeniyar Nukiliya
Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar Iran za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliya duk kuwa da ficewar Amurka daga cikinta amma da sharadin sauran kasashen Turai za su ci gaba da girmama ta sannan kuma Iran za ta cimma abin da ta ke so.
Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne a matsayin mayar da martani ga jawabin da shugaban Amurka Donald Trump yayi a daren jiya inda ya sanar da ficewar Amurkan daga yarjejeniyar nukiliya, inda ya ce bai yi mamakin wannan sanarwar ta shugaban Amurkan ba, yana mai cewa tuni ya umurci ministan harkokin wajen na Iran da ya fara tattaunawa da sauran kasashen Turai da suke cikin yarjejeniyar don jin matsayarsu kan lamarin.
Shugaban na Iran ya ce tun da jimawa gwamnatinsa ta tsara abubuwa da kuma hanyoyin da za ta bi wajen mayar wa Amurka da aniyarta matukar ta fice daga yarjejeniyar yana mai kiran al'ummar Iran da su kwantar da hankalinsu da cewa babu wani abin da zai faru don kuwa tuni gwamnatinsa ta tsara yadda za ta tinkari wannan karya alkawari na Amurka.
Kasashen duniya daban-daban dai suna ci gaba da Allah wadai da matsayar da shugaban Amurkan ya dauka na ficewa daga yarjejeniyar nukiliyan.