Pars Today
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran ya ce; taimakawa kasar Syria gwamnati da al’ummarta yana a matsayin gwagwarmaya ne wacce take abin alfahari.
Shugaban kasar Iran din ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar bakuncin takwaransa na kasar Syria, Basshar Assad wanda ya kawo ziyara Iran.
An shiga rana ta uku a atisayin da rundunar sojin ruwa ta kasar Iran ke gudanarwa a cikin tekun Fasha da tekun Oman har zuwa tekun India.
Ministan harkokin wajen kasar Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa; gwamnatin Amurka ta dauki dukkanin matakan da take ganin cewa za su iya durkusar da kasar Iran, amma dai ba ta iya cimma burinta ba.
A rana ta ukku na atisayen shekara-shekara wanda sojojin ruwa na kasar Iran suke gudanarwa a ruwan teku na yankin, sojojin sun cilla makamai mai linzami samfurin Cruise daga jirgin ruwa na karkashin ruwa tare da nasara.
Shugaban kungiyar Inginiyoyi a nan Tehran ya ce kasar Iran ta cimma yerjejeniya da gwamnatin kasar Siriya na gida gidaje dubu 200 a kasar ta Siriya
Sojojin kasar Pakistan sun jaddada azamarsu ta yin aiki tare da kasar Iran domin hana afakuwar wasu hare-haren ta’addanci.
Gwamnatin kasar Afrika ta kudu na shirin kara fadada harkokin kasuwancinta tare da kasar Iran.
A jiya rundunar sojin ruwa ta kasar Iran ta fara gudanar da wani gagarumin atisayi na tsawon kwanaki uku mai taken "Wilyah 97".